Jam’iyyun adawa a Liberiya sun ce za su shiga zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, duk da yake bas u amince da sakamkon farko ba.
Dan takarar day a zo na biyu, Winston Tubman da wasu ‘yan adawan sun fadi jiya Lahadi cewa za su janye umurnin kaurace wa zaben tun da ma sakamakon farko bai nuna cewa wani ya ci adadin kuru’un da ake bukata don kauce wa zaben zagaye na biyu ba.
To amman sun gargadi hukumar zaben kasar da cewa ta fa yi hattara, ta kauce wa duk wani magudi a zagaye na biyu na zaben, wanda za a gudanar ran 8 ga Nuwamba.
Bisa ga sakamako na baya bayan nan, Shugaba mai ci Ellen Johnson Sirleaf na kan gaba a zaben na makon jiya, da kuri’u kimanin kashi 45%. Shi kuma Tubman na da kimanin 31%, sannan tsohon shugaban ‘yan tawaye Prince Johnson ya sami kimanin 11%.
A wani jawabin da su ka yi ranar Asabar, jam’iyyun adawa 8 na Liberiya sun ce jami’an zaben sun murde sakamakon zaben don shugaba mai ci Sirleaf, ta yi nasara.
Hukumar zaben Liberiya dai ba ta mayar da martani kai tsaye ga zarge-zargen magudin ba. Ta dai yi kira ne ga dukkannin jam’iyyun su bi tsarin doka wajen gabatar da koke-kokensu.
Masu lura da zaben daga Kungiyar Kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS, sun ce zaben na ran 11 ga wata ya gudana cikin aldalci da gaskiya, kuma ana gudanar da kidayar salun alun.
Kungiyar mai zaman kanta ta Carter Center da ke da hedikwata a nan Amurka t ace wasu ‘yan kananan kura-kurai ne kawai ta gano.