Shugabar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf da wata ‘yarLiberiyar ‘yar gwagwarmayar zaman lafiya mai suna Leymah Gbowee da wata ‘yar Yemen ‘yar rajin kare hakkin mata Tawakkul Karman sun ci lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel ta 2011.
Kwamitin bayar da kyautar ta Noble da ke kasar Norway ne ya bayar da sanarwar a yau dinnan Jumma’a a birnin Oslo, da cewa matan uku za su raba muhimmiyar kyautar saboda salon gwagwarmayarsu ta kara lafiyar mata da hakkin mata cikin lumana.
Ciyaman din Kwamitin Thorbjoern Jagland ya yabi ayyukan mata ukun da aka basu kyautar, da cewa ba za mu sami zaman lafiya mai dorewa a duniya ba har sai mata suna samin irin sukunin da maza ke samu.
Ellen Johnson Sirleaf, ‘yar shekaru 72, ta zama mace ta farko da aka zaba shugabar kasa a dimokaradiyyance a nahiyar Afirka a 2005. Kwamitin bayar da kyautar ta Noble, ya yaba wa Shugabar ta Liberiya saboda kokarinta na samar da zaman lafiya, da kawo cigaban tattalin arziki da abubuwan more rayuwa da kuma inganta matsayin mata.
Leymah Gbowee yar shekaru 39, wadda ita ma ‘yar Liberiya ce, ta taimaka wajen kawo karshen yakin kasarta ta wajen sa matan Kirista da Musulmi yin zanga-zanga ta zama akai-akai ba tare da wani tashin hankali ba. A 2011, Gbowee ta sa matan Liberiya shiga yajin kaurace wa jima’i har sai an kawo karshen tashe-tashen hankula.
A halin da ake ciki kuma, Tawakkul Karman, ‘yar jarida mai shekaru 32 ta sami yabo saboda ficen da ta yi a gwagwarmayar kare ‘yancin mata da demokaradiyya da kuma tabbatar da zaman lafiya a Yemen.