Rundunar sojan Ivory Coast tace an kashe mutane goma sha biyar a sakamakon harin da wasu yan bindigan kasar Liberia suka kai ta kan iyaka. A jiya asabar wata kafar soja ta tabbatar cewa an kai harin ne a wani kauye dake kusa da kan iyakar Liberia.
Kafar ta fadawa kamfanin dilancin labarun Faransa cewa cikin wadanda aka kashe harda farar hula goma da wani soja da kuma uku daga cikin yan bindigan.
Yanzu haka dai kasar Cote D'voire tana farfadowa ne daga rikicin siyasa data kunno kai a karshen bara lokacinda tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo yaki, ya sauka daga kan ragamar mulki duk da cewa shugaban kasar na yanzu Alassane Ouattara ya kada shi a zaben shugaban kasa. Akalla mutane dubu uku ne aka kashe a tarzomar watani hudu na bayan zabe da aka yi.
Daruruwan sojojin haya da suka fafata domin Mr Gbagbo suna sansanoni a kasar Liberia.