A cigaba da ziyarce-ziyarcen jajantawa da na kaddama da ayyuka da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ke yi, yau ya ziyarci jahar Filato ta arewacin Najeriya, inda ya sauka filin jirgin saman Yakubu Gowon da ke Haifang daura da Jos, babban birnin jahar Filato da misalign karfe 12 na rana inda jama’a da dama daga sassa daban-daban da kuma jam’iyyu daban-daban su ka fito domin marabtar Shugaban na Najeriya.
Wakiliyar Sashin Hausa Zainab Babaji ta gaya ma abokiyar aikinmu Maryam Dauda cewa Shugaba Buhari ya kaddamar da ayyukan da su ka hada da hanyar Mararrabar Jama’a wadda ke hada Abuja da Filato da kuma sauran jahohin Najeriya. Buhari ya kuma kai ziyara Fadar Sarkin Jos (Gbong Gom Jos) inda su ka kebance cikin Fadar ba tare da ‘yan jarida ba.
Daga cikim abubuwan da Buhari ya je yi a Filato har da ganawa da masu ruwa da tsaki na bangarori daban-daban a jahar da zummar tabbatar da zaman lafiya tsakanin mabanbantan al’ummomi. A yayin da jama’ar jahar ke yaba ma Buhari kan yaki da almundahana da ya ke yi a kasar, su na kuma fatan zuwansa zai karfafa zaman lafiya tsakaninsu.
Wani abin da ya ja hankalin wakiliyar Sashin Hausa shi ne irin dafifin da jama’a su ka yi cikin birnin Jos don su ga Shugaba Buhuri.
Ga dai cikakkiyar hirar su Maryam da Zainab:
Facebook Forum