Yau Alhamis ce shugaban Amurka Barack Obama ya yi bulaguro zuwa New York domin ya karrama mutanen da harin ta’addanci ranar 11 ga watan satumban 2001 ya halaka.
Shugaban ya kai wannan ziyara ce, kwanaki bayan da dakarun Amurka suka kashe shugaban kungiyar Al-Qaida, Osama bin Laden a Pakistan.
Cikin ayyuka da shugaban ya yi har da aje furannin kallo a harabar cibiyar hada hadar kasuwanci ta Duniya da harin ya rusa, san nan daga bisani ya gana da iyalan wadanda harin ya rutsa dasu. Fadar shugaban Amirka ta White House tace shugaban na Amurka ba zai yi wani jawabi a bainar jama'a ba.
Shima mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden, a yau Alhamis ya karrama wadanda harin na 11 ga watan satumban ya halaka a wani bikin aje furanni a wani dandalin tunawa da wadanda suka halaka ranar, a ma’aiikatar tsaron Amurka da ake cewa Pentagon.