Shugaba Alassane Ouattara da Nana Akufo-Ado na kasar Ghana, sun gana a sirince. Shugaban kasar Ghana yayi godiya da amsar goron gayyata da shugaba Akufo-Ado yayai, ya kuma yi bayanin cewa kasashen biyu zasu samu Alkhairi da dama bayan sakamokon hukuncin kotu na kasa da kasa na shari’ar ruwan teku.
Shugaban Ghana ya jinjinawa bakon nasa shugaba Ouattara akan dattaku da ya nuna bayan bayyana sakamokon shari’ar, Ya kara da cewa a yayin shari’ar sun fahimci cewa sun shiga mawuyacin hali tsakanin su da Cote d’Ivoire, amma sun yi amfani da wannan a matsayin ginshikin kara karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
A bangaren shugaba Alhassan, kuma ya nuna matukar godiyarsa ga shugaban kasar na Ghana game da wannan gayyata da kuma nuna godiyar sa musamman kan yadda kasar ta Ghana ta karbi ‘yan gudun hijirar kasar Cote d’Ivoire, a yayin da kasar ta shiga wani hali a kawanakin baya.
Kasashen biyu dake gaba wajan noman koko, a duniya sun kulla wata yarjejeniyar hadin gwiwa da zata basu damar cin gajiyar zufar su.
Dag Ghana ga rahoton da Ridwan Abbas ya aiko mana.
Facebook Forum