Dr Andiya Abdullahi, kwararre akan cutar dajin jinni, ya shaidawa wakilin Muryar Amurka dake Yamai, Souley Barma, cewa mutane fiye da dari biyu suke fama da cutar. A cewarsa, cikin ‘yan kwanakin nan mutane bakwai suka rigamu gidan gaskiya sanadiyar cutar.
Masu fama da cutar sun hada gwuiwa da likitoci domin kafa wata kungiyar yaki da cutar ta hanyar fadakar da jama’a.
Malam Bukari Aliyu, shugaban rikon kwarya na kungiyar, ya ce cuta ce da take bukatar ana gwajin jini a koda yaushe, musamman bayan kowane watanni uku-uku.
Manufar kungiyar dai ita ce yadda zata taimakawa masu karamin hali su samu suna gwajin jini lokaci lokaci. Abu na biyu shi ne kula da wadanda ‘yanuwansu ma sun riga sun yi watsi dasu, basa kula da su.
Dr. Andiya Abdullahi yace alamomin cutar guda hudu sun hada da gajiya, ramewa, yawan futsari da kuma fitar da wani kololo ta hannun hagu.
Maganin dajin jini na da matukar tsada, lamarin da kan gagari talakawa da mara sa karfi.
Amma a dalilin sabuwar kungiyar yaki da cutar, har an fara samun magungunan cutar kyauta daga wata kungiya dake kasar Amurka.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani
Facebook Forum