Za a gudanar da zagaye na biyu a zaben Shugaban kasar Liberiya, a tsakanin shahararren tsohon dan wasan kwallon kafan nan George Weah da kuma Mataimakin Shugaban kasa na yanzu Joseph Boakai, a cewar Hukumar Zaben Kasar a jiya Lahadi.
Bayan kidaya wajen kashi 95% na kuri'un da aka kada a wannan kasa ta Yammacin Afirka, Weah ya samu kashi 39% a yayin da shi kuma Boakai ya samu kashi 29.1%. Wannan na nuna cewa ke nan babu daya daga cikinsu da ya sami adadin da ake bukata na kashi 50% kafin a zama Shugaban kasa, a zagaye na farko na zaben na makon jiya.
Masu zabe miliyan 2.1 da su ka yi rajista a kasar ne suka kada kuri'ar zaben wanda zai gaji Ellen Johnson Sirleaf, mace ta farko da ta zama Shugabar kasa a Afirka, wacce za ta sauka bayan ta ciki wa'adi biyu masu tsawon shekaru shida-shida, kamar yadda kundin tsarin mulkin Liberia ya tanada.
Facebook Forum