Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Masar Sun Dakile Wani Shirin Kai wa 'Yanuwansu Hari a Yankin Sinai


Shugaban Masar Abdel-Fattah el-Sissi
Shugaban Masar Abdel-Fattah el-Sissi

Kwana guda bayan wasu 'yan tawaye sun kashe wasu 'yan sanda a yankin Sinai kasar Masar, sojojin kasar sun dakile wani sabon shirin kai wa sojojin dake yankin sinai din hari

Sojan Masar sun bata wani yunkuri da wasu 'yan bindiga suka yi na kai hari kan wasu na'urorin soji a yankin Sinai, kwana guda bayan da 'yan tawayen su ka kashe wasu 'yansanda a yankin, a cewar wata sanarwa ta soji.

Sanarwar Rundunar sojin Masar ta ranar Asabar ta ce wasu gungun 'yan tawaye sun kutsa cikin wani barikin soja maimatukar matakan tsaro a birnin el-Arish da ke arewacin Sinai don kai wani harin ta'addanci.

Mayakan, wadanda su ka yi shigar burtu da kayan sarki irin na sojin Masar, na dauke da gurnet-gurnet da bindigogi da kuma gurayen bama-bamai da akan yi amfani da su wajen kai harin kunar bakin wake, a cewar mai magana da yawun sojojin Masar, Tamer El-Refaie, a cewar sanarwar.

Rafaie bai fadi adadin 'yan bindigar da aka kashe ba. To amma akalla wani dan bindiga ya mutu bayan da bam din da yayi damara da shi ya tashi.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG