Dakta Abdulkadir Adam, shugaban ma’aikatar kula da motocin daukar marasa lafiya na gaggawa, ya fadawa sashen Somaliyanci na Muryar Amurka cewa izuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 302, daga mummunar fashewar da ta faru a wata mahada mai yawan hada-hadar mutane a yammacin ranr Asabar.
Gwamnatin Somaliya ta ce an ‘dauki mutane 429 da suka samu raunukkazuwa asibitocin yankin, haka kuma akwai yiwuwar karuwar yawan mutanen da suka mutu. Sama da mutane 30 dake cikin mawuyacin hali ne aka kwashesu zuwa assibitocin kasar Turkiyya a jiya Litinin don duba lafiyarsu, cikinsu harda wakilin Muryar Amurka a Somalia, Abdulkadir Mohammed Abdulle.
Ya zuwa yanzu dai babu wani ko wata kungiyar da ta fito ta dauki alhakin harin, amma jami’an gwamnati da kwararru kan harkar ta’addanci sun yi imanin cewa kungiyar al-Shabab ce ta kitsa kai harin.
Ita kanta Kungiyar al-Shabab dai ta yi shiru akan wannan hari, amma an san cewa ta jima tana kashe daruruwan mutane a yan shekarun da suka gabata ta hanyar kai hare-hare akan otel-otel na Magadishu da gidajen cin abinci da kuma sauran guraren da jama’a ke hada-hada.
Facebook Forum