Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Birtaniya Ta Kori 'Yan Diflomasiyar Rasha Daga Kasarta


 Theresa May, Firayim Ministar Birtaniya
Theresa May, Firayim Ministar Birtaniya

Firayim Ministar Birtaniya Theresa May ta mayarwa Rasha martani akan harin guba da ta kai Birtaniya kan wani dan asalin Rasha kuma tsohon dan leken asiri da yake zaune a Ingila da diyarsa da yanzu su biyun rai na hannun Allah

Birtaniya ta sanar da daukar matakan maida martani kan Rasha da suka hada da korar jami’an diplomasiyan kasar Rasha ishirin da uku, bayanda Rasha tayi watsi da bukatar da Birtaniya ta gabatar na neman bayani dangane da yadda aka iya yin amfani da sinadarin guba mai mummunan karfi da rasha ta sarrafa a zamanin mulkin Soviet, a garin Salisbury kan tsohon jami’in leken asirin kasar Rasha Sergei Skirpal da yarsa Yulia.

Firai minister Birtaniya Theresa May ta sanar da daukar wannan matakin a zauren majalisa da ya cika makil. Ta sanar da cewa, gwamnatinta zata shata daftarin da zai kare al’ummar kasar daga duk wata barazana, zata kuma yi nazarin daukar sababbin matakan yaki da liken asiri kasa. Matakan maida martanin da zata dauka sun hada da amfani da yin wadansu gyare gyaren a dokokin takunkumi da zasu bada izinin hana ‘yan kasar Rasha da aka hakikanta suna keta hakkin bil’adama amfani da kaddarorinsu, da kuma soke huldar manyan jami’an gwamnati tsakanin Birtaniya da Rasha da suka hada ziyarar da ministan harkokin kasashen ketare na kasar Rasha Sergey Lavrov, ke shirin kaiwa Birtaniya.

An ba Rashawan da aka kora mako guda su fice daga Birtaniya a wani abinda aka bayyana a matsayin korar jami’an diplomasiyan kasar Rasha mafi girma tun shekara ta dubu da dari tara da saba’in da daya, lokacin yakin cacar baki.

Rasha ta musanta cewa tana da hannu a kai harin gubar, ma’aikatar harkokin wajen kasar kuma tace, jawabin da May tayi jiya, takala ce da ta toshe kafar tattaunawa tsakanin kasashen biyu. Ta kuma kara da cewa, Rasha zata maida martani nan ba da dadewa ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG