Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saudi Arabiya Zata Kera Makamin Nukiliya Muddun Iran Ta Kera


Yarima Mai Jiran Gado, Mohammed bin Salman
Yarima Mai Jiran Gado, Mohammed bin Salman

A ci gaba da jayayyar da ake yi tsakanin Saudiyya da Iran, Saudiyya ta ce muddun kasar Iran ta kera makamin nukilya to ita ma za ta kera.

Yerima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed Bin Salman, ya kira shugaban Malaman addinin Iran "Hitila" (Hitler), ya ce kasar Saudiyya ma zata kera makaman Nukiliya muddin Iran ta kera.

"Saudiyya bata da niyyar mallakar makaman Nukiliya, amma ba tareda wani kokonto ba, idan Iran ta kera makamin Nukiliya, muma zamu bi sawu, ba tareda bata wani lokaci ba," inji Yerima Mohammed, a wata hira da tashar talabijin ta CBS dake Amurka tayi dashi, kuma za'a nuna wa duniya a cikin shirin da ake kira "60 minutes" da turanci, a ranar Lahadi idan Allah ya kaimu.

A dandanon hirar da tashar ta fitar a yau Alhamis, Yeriman yace, yadda ake tunkarar shugaban Iran, dai dai yake da yadda duniya ta tunkari Hitler, lokacin da akidar Nazi take tashe a Jamus.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG