Wakilai daga kasashen nahiyar Afrika suna halartar taron kungiyar Commonwealth a birnin London da taken “abinda ya shafi kowa”.
Batutuwan da za a tattauna a kai sun hada da, sauyin yanayi da inganta damawa da kowanne jinsi.
Maria Fernandez De la Vega, shugabar cibiyar matan Afrika ce ta gabatar da jawabin bude taron.
Tace a wannan lokaci da ake fuskantar rashin ba kowa dama ta bai daya, tilas ne mu ci gaba da tada muryarmu a kan wannan batun. Tace hada hannun matasa da kuma mata zai bamu damar maida hankali kan Afrika.
Cibiyoyi kamar MDD da kuma KTA suna Magana a kan batun bada dama ta bai daya ga kowanne jinsi.
Kasashen kungiyar commonwealth, kasashe renon ingila ne, Birtaniya kuma tana kokarin sake kulla dangantaka da kasashen musamman a wannan lokacin da ta fice daga KTT.
Facebook Forum