Shugaban Amurka Donald Trump yana maraba da yiwuwar dakatar da ayyukan gwamnati in har majalisar dokokin kasar ba ta goyi bayan shirinsa na yin garambawul a fannin dokokin shige da fice ba.
Trump ya kara da cewa, “rufe gwamnatin” alheri ne ga kasar idan dai akan wannan batu ne.
Mr. Trump ya furta hakan ne a lokacin wani taro a jiya Talata tare da wasu jami’an tsaro da ke maida hankali akan batun ‘yan kungiyar tsagerun da ake kira Mara Salvatrucha, wadda aka fi sani da suna MS-13.
Trump ya sha nanata laifukan da baki ke yi a duk lokacin da yake jaddada muhimmancin yin garambawul a dokokin shige da fice na Amurka.
Ya akra da cewa, yin kwaskwarima a wannan fannin, zai inganta tsaro a bakin iyakar kasar, da kawo karshen shigo da baki ta hanyar iyali, da kuma dakatar da ba da takardar zama dan kasa ta hanyar canki-cankin gasar Lottery.
Shugaba Trump yana mai muradin ganin an yi amfani da cancanta idan za a bar baki su shiga Amurka.
Facebook Forum