Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Donald Trump Yace Zai Yi Maraba Da Sabon matakin Rufe Ayyukan Gwamnati


Donald Trump
Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a jiya Talata cewa zai yi maraba da sabon matakin rufe harkokin gwamnati idan majalisun kasar sun gaza cimma matsaya a kan daukan karin tsauraran matakai a kan bakin haure.

Trump yace yana sha’awar ganin rufe ma’aikatun gwamnati idan an kasa samun daidaito.

Kira ga yiwuwar rufe harkokin gwamnati da Trump yayi, ta biyo bayan fafitukar da wakilan majalisa suka sha wurin tabbatar da karin lokacin kashe kudaden gwamnati, kwanaki biyu kafin shirin kashe kudaden gwamnatin na wucin gadi ya zo karshe a cikin daren gobe Alhamis.

An samu rufe harkokin gwamnati na tsawon kwanaki uku a cikin watan Janairu a karo na farko, tun bayan wanda ya faru a shekarar 2013, wanda shima ya ta’alaka a kan irin wannan batu na bakin haure.

A wata sanarwa da ta biyo baya, fadar White House tace zata marawa shirin gudanar da harkokin gwamnati na wucin gadi ya zuwa 23 ga watan Maris, domin ba wakilai karin lokacin tattauanawa a kan yarjejeniyar bakin hauren.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG