Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Hakikance Rasha Zata Cika Alkawarin Rage Makaman Nukiliya


Rex Tillerson, Sakataren Harkokin Wajen Amurka
Rex Tillerson, Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Ta Ce Rasha Zata Cika Alkawarin Rage Makaman Nukiliya bisa yarjejeniyarsu da suka rabtabawa hannu a shekarar 2010 da aka lakabawa START

Amurka ta hakikance cewa Rasha zata cika alkawarin da ta yi a karkashin yarjejeniyar da aka yi ta rage amfani da makaman Nukiliya da ake kira START a takaice, daga yau Litinin tunda itace rana ta karshe da aka tsayar domin yin hakan.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi cewa , duka kasashen biyu zasu ci gaba da baiwa juna bayanai akan makaman kare dangin da suke dasu "a cikin wata mai zuwa, kamar yadda muke yi sau biyu a duk shekara, cikin shekaru bakwan da suka gabata, bisa yadda yarjejeniyar ta tsara."

An sakawa sabuwar yarjejeniyar ta START hannu a ranar 8 ga wata Afrilun shekarar 2010 a birnin Prague, kuma aka fara aiwatar da ita a watan Febrairun 2011.

Yarjejeniyar ta kayyadewa Rasha da Amurka makaman nukiliyan da zasu iya mallaka inda ta ce baza su wuce 1,550 ba, hakan ta rage yawan makamai masu linzami da aka dana, da wadanda ba'a dana ba masu cin dogon zango.

Kwararru sun ce duk da banabance banabancen dake akwai tsakanin Rasha da Amurka akan katsalandan din da aka ce Rasha tayi a Zaben Amurka, da rikicin Syria, da kuma Ukraine da sauran batutuwa, ganin yadda duka bangarin suke hada kai wajen sa ido da tanatance alamuran nukiliya, babban abu ne ga tsaro da kwanciyar hankalin duniya.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG