Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Wanene Ya Cancanta Ya Zama Shugaban Najeriya a Zaben 2015


Shugaba Goodluck Jonathan
Shugaba Goodluck Jonathan

Shugaban kungiyar yayata manufar shugaba Jonathan Otunda Basirat Naibi ta nisanta shugaban da batun tabarbarewar tsaro a kasar inda take cewa shugancin kasa daban, harkokin tsaro kuma daban ne.

Tayi jawabi a wani babban gangamin taron neman zaman lafiya na yankin arewa maso yamma da kungiyar ta gudanar a Sokoto.

Amma taron ya juye ne ya zama taron yayata manufofin shugaban kasa Goodluck Jonathan tare da nema masa goyon baya a fafitikarsa ta neman zarcewa a wa'adi na biyu na shugabancin Najeriya bayan da jam'iyyarsa ta PDP ta amince masa tsayawa takara.

Onarebul Danladi Baido babban sakataren kungiyar na kasa yace mutane suna daukar siyasa suna hadata da maganar zaman lafiya. Siyasa daban kuma maganar zaman lafiya daban take. Idan duk 'yan siyasar kasar zasu hadu su nemi zaman lafiya to duk maganar cewa Goodluck Jonathan ya kasa akan harkokin tsaro ba zai taso ba.

Mataimakin gwamnan jihar Sokoto Barrister Mukhtari Bala Shagari wanda ya raba gari da gwamnan jihar a siyasance yana ganin shugaba Jonathan na binsu bashi wanda ya wajaba su biyashi. Yace da maigirma gwamnan Sokoto dashi Bala Shagari shugaba Jonathan na binsu bashi domin ya goya masu baya a zaben 2011. Yace idan su ba butulai ba ne to shi da gwamna sai su goya mashi baya, Sakwatawa kuma su jefa mashi kuri'a. Yace sabo da haka Allah shi ya hada Kirista da Musulmi cikin kasa guda mai suna Najeriya. Idan kuma akwai wani gagarumin dan siyasa da yace Allah bai iya ba sai ya fito ya fada masu.

A wani bangaren kuma hadakar kungiyoyin matasa na jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara ta gudanar da irin wannan taron inda ita kuma ta nuna goyon bayanta da tsayawar takarar mataimakin tsohon shugaban Najeriya Atiku Abubakar a karkashin inuwar jam'iyyar adawa ta APC.

Mai magana da yawun kungiyoyin Usman Afan yace sam Shugaba Jonathan bai cancanci shugabancin kasar a karo na biyu ba saboda kasawa da shugaban yayi a wa'adin mulkinsa na farko. Yace yanzu halin da Najeriya take ciki, ba ma dan arewa ba kawai har da dan kudu ya damu da yanayin da kasar ke ciki ta harkar tsaro. Ta hanyar arziki mutane sun tagayyara suna bukatar canji. Idan Jonathan y a yiwa kansa adalci zai yi hakuri ya bar mulkin domin a zauna lafiya.

Dangane da marawa Atiku baya maimakon Janaral Buhari sai Usman Afan yace ba wai sun tsaya akan mutum guda ba ne. Sun san Atiku kuma sun san Buhari. Amma yanayin siyasa yanzu abubuwa sun canza Atiku ya fi dacewa.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG