Shawarar da jam’iyyar PDP ta yanke cewa Shugaba Goodluck Jonathan ne dan takararta na zaben Shugaban kasa a 2015 na tayar da muhawara tsakanin masu ganin hakan daidai ne da wadanda ke ganin hakan bai dace ba.
Wakilinmu a Abuja Saleh Shehu Ashaka ya ruwaito wani dan PDP mai suna Shu’aibu Badegi daga jihar Naija na cewa wasu ‘yan boko ne ke haddasa rudami tsakanin ‘yan Nijeriya, alhalin ko ‘ya’yansu ma ba su makaranta a Nijeriya. Don haka, a cewarsa shi, a 2015 zai zabi Shugaba Goodluck Jonatan ne.
Shi kuma Jauro Hammadu daga jihar Gombe ya gaya wa Saleh cewa koma wa jam’iyyar PDP ta tsayar shi zai ci zaben saboda ita ta fi karfi da yaduwa a sassan Nijeriya.
To amma wani dan kasuwa mai suna Saleh Garkuwa ya ce shi fa gani ya ke Shugaba Jonathan so kawai yake ya dauwama kan karagar mulki saboda take-takensa sun yi kama da wata dabarar da aka taba amfani da ita a Tarayyar Soviet don yin tazarce.
Saleh ya ce wasu kuma masu ganin Shugaba Goodluck Jonathan so ya ke ya yi Shugabancin Nijeriya wa’adi na kuma, abin da su ka ce bai dace ba, su na shirn rugawa kotu.