Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rushewar Runfa Ta Rage Armashin Gangamin Kiran Jonathan Ya Yi Takara a 2015


Gwamna Mu'azu Babangida Aliyu.
Gwamna Mu'azu Babangida Aliyu.

Rushewar Rumfa Ta Rage Armashin Gangamin Kiran Jonathan Ya Yi Takara a 2015. To amma ba a rasa rai ba.

Rumfa ta rushe kan gagga-gaggan ‘yan jam’iyyar PDP yayin wani taron gangamin nemar Shugaba Goodluck Jonathan ya tsaya takarar Shugabancin Nijeriya a 2015.

Wadanda abin ya rutsa da su sun hada da mai masaukin baki gwamna Mu’azu Babangida Aliyu na jihar Naija da Gwamnan jihar Kogi da Ministan Labarai Labaran Maku da Mataimakin Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Muntari Shagari da wasu Sanatoci da dai sauransu. Wakilinmu na Mina Mustapha Nasiru Batsari y ace cikin wadanda su ka sami raunuka hard a matar gwamman jihar Naija.

Mustapha y ace kodayake rushewar rumfar bat a hana cigaba da taron ba, akasarin mahalarta taron sun watse bayan rushewar rumfar. Y ace wasu ‘yan jam’iyyar ma na ganin mugunta aka masu. Hasali ma wani dan jam’iyyar mai suna Usman Direkta y ace gwamna Babangida Aliyu aka auna a muguntar. To amma kuma ya amince cewa hakan na iya zama alhakin talakawa.

To amma a nasa martanin, Gwamna Mu’azu Babangida Aliyu y ace kaffara ce. Don haka ya yi kira ga jama’a da a cigaba da taro.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG