Duk da cewa 'yan Najeriya da kungiyoyi suna ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu dangane da halaccin wannan kwamiti, tuni wasu mutane da kungiyoyin daga bangarorin kasar suka bayyana goyon bayansu kan kudurin kwamitin.
Wani lauya mai zaman kansa, Yusha'u Waziri Mamman yace sashe na 17 da 19 da wasu sassa daban daban na tsarin mulkin kasa sun baiwa shugaban kasa ikon kafa irin wannan kwamiti idan har ya hakikance cewa hakan zai taimakawa ci gaban kasa da zaman lafiya.
Ga karin bayani.