Kafin Kakakin rundunar 'yan sandan jahar Kanon ya yiwa Bello Habeeb Galadanchi bayani, wakilin Sashen Hausa a Kano Muhammad Salisu Rabiu ya bayar da bayanan farko-farko inda ya ce wani dalibi ya shaida mi shi cewa a wajen ajiye motoci aka boye bom din da ya tashi:
Bayan wannan bayani na wakilin Sashen Hausa Muhammad Salisu Rabiu, shi ma Anas Saminu Ja'en wani shaida dake tsaye a bakin makarantar ya ganewa idon shi yadda aka fitar da wadanda harin ya rutsa da su, ya ce da idon shi ya ga an fitar da kimanin mutane goma jina-jina.
Kakakin rundunar 'yan sandan jahar Kani A.S.P Magaji Musa Majiya ya ce bayan an kwashe wadanda harin ya rutsa da su, masanan kwance boma-bomai sun kara duba ko'ina ko da wani bom a makale a wurin, amma ba su gani ba. A.S.P Magaji Musa Majiya an kama wani mutumin da aka ga alamun rashin gaskiya tare da shi, wanda kuma tuni aka tuhuma da hannu a cikin kai harin. Kuma Ya kara da cewa kwamishinan 'yan sandan jahar Kano ya sa a zafafa sintiri a makarantun Kano, kuma su na ci gaba da daukan matakai daban-daban, da na fili, da na boye domin kare rayukan jama'ar jahar Kano.