Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Menene Manufar Koriya ta Arewa Kan Wargaza Shirin Nukiliyarta?


Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un

Duk da karfin gwuiwar da shugaban Amurka Trump yake dashi akan abun da zasu cimma da shugaban Koriya ta Arewa ana sa ran yakamata Koriya ta Kudu ta sana manufar Koriya ta Arewa akan shirin wargaza nukiliyarta musamman a zirin dake tsakanin kasashen

Yayin da ake jiran taron kasashen Koriyoyin nan biyu a karshen wannan watan , ana sa ran kasar Koriya ta Kudu ta nemi cikakken bayanin abinda wargaza shirin makami mai linzami na kasar Koriya ta Arewa ke nufi a yankin zirin na Koriya, inji tsoffin jami’an Amurka da suka yi hulda da Koriya ta Arewa na tsawon lokaci.

Sai dai yayin da shugaba Trump ke da kwarin gwuiwa game da tattaunawar da zasu yi da shugaban na Koriya ta Arewa Kim Jong Un, wadannan tsoffin jami’an na Amurka suna tabbatar cewa Amurka da Koriya ta Arewa sun fahimci juna akan ma’anar wargaza ko kuma dakatar da shirin makami mai linzami na kasar ta Koriya ta Arewa.

Jami’an Amurka sun tabbatar a aranar Asabar cewa Koriya ta Arewa ta fada wa fadar White House kai tsaye cewa Shugaba Kim zai yi sha’awar tattaunawa kuma a shirye yake ya tattauna shirin dakatar da dukkan abinda dake da alaka da tsarin sa na makami mai linzami, idan sun hadu a wurin tattaunawa da shugaba Trump.

A ranar Littini ne dai Trump yace yana tsammanin cewa za a samu kyakkyawar fahimtar juna a sakamakon wannan tattaunawar kuma hakan zai kawo wargaza makaman nukiliyan Koriya ta Arewa.

Trump yace zai gana da Kim a karshen watan Mayu ko kuma farkon watan Yuni.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG