Fadar shugaban Koriya ta Kudu ta ce a yau Litinin ne shugaba Moon jae-in zai aike da wata tawaga mai karfin gaske zuwa Korea ta Arewa, domin tattauna yadda kasashen biyu zasu inganta dangantaka, da rage zaman tankiyar da ake yi tsakanin su.
Tawagar ta musamman zatayi tattaunawa mai zurfi akan muhimmam batutuwa ciki ko har da wanzar da yanayin da za a iya yin tattaunawa cikinsa a tsakanin Koriya ta Arewa da Amurka, mai Magana da yawun shugaba Moon, Yoon Young-Chan ya shaidawa manema labarai.
Sai dai wannan yunkurin na iya fuskantar matsala a saboda wani atusayen sojan hadin guiwa da aka shirya gudanarwa a tsakanin Amurka da Koriya ta Kudu, inda har Koriya ta Arewa ke gargadin cewa hukumomi a Pyongyang zasu dauki matakan mayar da martani ga Amurka muddin aka gudanar da wannan atusaye a watan Afrilu.
Facebook Forum