Kungiyar ta fitar da wani sanarwa ta yanar gizo tana cewa zata fitar da wasu sabbin dabarun kai hare-hare kan kamfanonin dake hako man fetur a yankin.
Baicin hakan kungiyar ta ba kamfanonin hakan mai da su kwashe nasu inasu su bar kasar tunda wuri ko kuma su hadu da fushinta. Sanarwar ta kara da cewa zasu fara kakkabo jiragen sama masu saukar angulu dake shawagi a yankin nasu daga ranar bakwai ga watan Yulin wannan shekara. Sun kara da cewa sojojin Najeriya ba sa iya hanasu kai hare-hare a duk lokacin da suka so da inda suka so.
Kungiyar ta yi ikirarin kashe wasu sojoji uku tare da nitsar da wasu da dama, wai, a lokacin wani artabu.
Janar Rabe Abubakar daraktan watsa labarai na rundunar sojin Najeriya ya bayyana irin matakin da suke dauka domin tunkarar wannan lamarin. Yace barazana ce wasu 'yan tsiraru da suke ganin ba'a yi dasu suke kai hari. Suna son su tilastawa 'yan Najeriya cewa sai an yi dasu. A zamansu na sojoji yace ba zasu razana ba. Yace su kansu tsagerun, 'yan yankinsu sun la'ancesu.
Janar Rabe yace masu aikata ta'asar 'yan yara ne da basu san abun da suke yi ba.
Ga karin bayani.