WASHINGTON, DC —
Kotun da ta zauna da karfe tara na safe ta dage karar zuwa ranar ashirin da biyu ga wannan watan, hakan ya biyo bayan tafiya halartar wani taron bita da alkalin kotun yayi.
Manjo Al-Mustapha yace ”indan ka duba kazazzafen dake cikin kaset-kaset da shi wanda muka kai kara yayi tayi watanin da dama da suka wuce, maganganu masu nauyin gaske ne, inda ana maganar hakkin dan Adam, ana maganar gaskiya bisa yanda Allah ya shinfida a shariar Musulunci abune masu nauyi, so barin su ya wuce batare da an tuntubi hakan ba, barnane ga musulunci da musulmi da kuma kasa.”
Shi kuma Sheikh Khalid cewa yayi “to Alhamdulilahi mun zo ba’a samu sharia ba, domin komai sai Allah yayi, akance lokaci kaza, lokaci na Allah ne saboda haka Allah Bai hukuntar za’ayi shariar a yau ba, an daga sai ashirin da biyu ga wata, to kan wannan al-amari bazan ce komai ba tunda mun riga mun zo kotu sai abunda kotu ta yanke in Allah yaso kuma ya yarda."
Lauya Sadau Garba, mai kare wanda ya kai kara ya fadi dalilin zuwa kotu “karan da muke masa na kazafi ne da bata ma mai kara suna, a cikin hudubar da yake yi an kuma buga a kaset-kaset da DVD inda yake cewa gwamnati ta baiwa Al-Mustapha kwangila na horas da wasu yara,d omin a kashe mutane dubu a Najeriya saboda cin burin siyasar Goodluck Jonathan."
Shi kuwa Lauya Aminu Dikko dake kare wanda aka kai kara cewa yayi sunanan suna jira zuwa ranar da aka sa domin ci gaba da wannan sharia kuma zasu zo da hujojinsu.