Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Senegal Ta Shirya Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Ranar 24 Ga Maris


Shugaban Senegal Macky Sall - Picha na Seyllou / AFP.
Shugaban Senegal Macky Sall - Picha na Seyllou / AFP.

Shugaban Senegal Macky Sall ya shirya gudanar da zaben shugaban kasa da aka jinkirta ranar 24 a ga watan Maris, kamar yadda gwamnatin kasar ta bayyana ranar Laraba bayan da wata babbar kotu ta yanke hukuncin cewa shawarar gudanar da zaben bayan wa'adinsa ya kare ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Sanarwar ta zo ne da maraice yayin da Sall ya rushe gwamnati tare da maye gurbin Firayim Minista Amadou Ba da MMinistan cikin gida Sidiki Kaba domin ya ba Firayim Minista Amadou Ba, dan takarar Shugaban kasa na jam'iyya mai mulki, damar mayar da hankali kan yakin neman zabensa, in ji fadar shugaban kasar.

Tun da farko dai Majalisar tsarin mulkin kasar ta yanke hukuncin cewa shawarar da kwamitin tattaunawa na kasa ya bayar na kada kuri’ar da za a gudanar a ranar 2 ga watan Yuni ba ta yi daidai da kundin tsarin mulkin kasar ba.

Matakin dai shi ne na baya-bayan nan a rikicin zaben da aka shafe wata guda ana yi wanda ya haifar da tarzoma da kuma gargadi daga kawayen Senegal na kasa da kasa cewa suna fuskantar barazana a matsayinta na daya daga cikin tsayayyen kasashen dimocradiyya na yammacin Afirka da aka yi juyin mulki.

‘Yar takarar Shugaban kasa ta jam’iyyar adawa, Anta Babacar, wacce ke cikin mafi rinjayen ‘yan takara 19 da ke neman a gudanar da zaben da wuri ta yi na’am da sabuwar ranar zaben.

"Ina ganin wannan labari ne mai dadi sosai. Wannan shi ne dalilin da ya sa muke fafatawa a wadannan makonni da kwanaki da suka gabata, domin mun san cewa lalle za a iya gudanar da wadannan zabukan kafin ranar 2 ga Afrilu," kamar yadda ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Rikicin ya samo asali ne a yunkurin da hukumomi suka yi a farkon watan Fabrairu na dage zaben ranar 25 ga watan Fabrairu zuwa Disamba. Sall ya bayyana damuwarsa game da rigingimun zabe, sai dai wasu 'yan adawar sun ce hakan tamkar wani yunkurin juyin mulki ne na hukumomi.

Akalla mutane 40 ne aka kashe a rikicin da ya barke tun watan Maris din shekarar 2021 ba tare da hukunta masu hakkin ba, a cewar HRW.

Yawancin tashe-tashen hankulan siyasa sun samo asali ne saboda damuwar cewa Sall na ƙoƙarin murƙushe abokan hamayyarsa tare da riƙe madafun iko bayan ƙarshen wa'adinsa, lamarin da ya musanta.

Wata sabuwar zanga-zanga ta barke a watan jiya bayan da ya bayyana shirin dage zaben.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG