WASHINGTON, D. C. - Matakin dai ya biyo bayan sanarwar dage zaben da ba a taba ganin irinsa ba da shugaba Macky Sall ya yi a ranar Asabar din da ta gabata, wanda ya jefa kasar Afirka ta Yamma cikin wani rudani a mulkin kasar da kuma yin barazanar kara bata sunanta a matsayin wani tushe na tabbatar da dorewar demokradiyya a yankin da juyin mulki ya daidaita.
'Yan sandan kwantar da tarzoma sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zangar a wajen majalisar dokokin kasar yayin da 'yan majalisar ke tattaunawa kan kudirin dokar da, da farko ta gabatar da shawarar sauya ranar 25 ga watan Fabrairu zuwa ranar 25 ga watan Agusta da kuma ci gaba da rike Sall a kan karagar mulki har sai an nada sabon shugaba.
Ya zuwa yamma, gabanin kada kuri’a na karshe, an yi wa kudirin gyaran fuska, domin gabatar da ranar zaben ranar 15 ga watan Disamba, amma ‘yan majalisa 105 ne suka amince da shi a majalisar mai kujeru 165.
Gyaran da aka yi a minti na karshe na dage zaben zuwa Disamba maimakon watan Agusta na iya haifar da ci gaba da mayar da martani ga 'yan adawa tare da yin kasadar sake samun tarzomar zanga-zangar da ta barke cikin shekaru ukun da suka gabata a wani bangare na zargin Sall da cin zarafi.
Dage zaben ya fuskanci koma baya a wani bangare ranar Litinin. Akalla uku daga cikin 'yan takarar shugaban kasa 20 sun gabatar da kalubalen shari'a ga jinkirin, a yadda takardun Majalisar Tsarin Mulki suka nuna. Wasu ‘yan takara biyu sun sha alwashin kalubalantarsa ta hanyar kotu.
Kimanin mutane 100 ne suka taru a wajen majalisar a ranar Litinin, bayan arangama a ranar Lahadi, suna rera taken "Macky Sall mai kama-karya". ‘Yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye, inda suka bi su kan titunan gefe gari tare da kama wasu.
Hukumomin kasar sun hana shiga yanar gizo ta wayar hannu na wani dan lokaci daga daren ranar Lahadi, saboda sakonnin tashin hankali a shafukan sada zumunta da kuma barazana ga zaman lafiyar jama'a. Makarantu da yawa sun tura yara gida da wuri.
Tashar talabijin ta Walf mai zaman kanta ta ce an dauke aikinta ne a ranar Lahadi kuma aka kwace lasisin ta.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna