Ita kuwa Aisha Sarka, mai goyon bayan tsohon gwamnan cewa tayi “Mallam Ibrahim Shekarau yana tare da jama’a dari bisa dari, idan hagu yace hagu, idan dama yace dama.”
Tuni dai shuwagabanni da magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar Kano suke tsalle da murna, dangane da tagomashin da jam’iyyar tasu, suka ce ta samu.
Alhaji Musa dan Birni yace “Sai muka ji dadi, mun yi Wa Allah godiya kuma jam’iyyata ta PDP ta rabauta yau da babban kamu na Mallam Ibrahim Shekarau. Shigowarsa wannan jam’iyya tawa, ta samu tagomashi kasancewarsa mutumin mutane.
Amma ‘ya’yan APC suma sun tofa albarkacin bakinsu, dangane da wannan sauyin sheka da tsohon gwamnan yayi. Mallam Rabi’u Abdullahi Garin Danga, na hannun daman gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso yace “yau dinnan a siyasance, Mallam Ibrahim Shekarau ya fassara kansa a wajen mutanen Kano a siyasance.”
Mallam Garin Danga ya jaddada zargin da ake wa Mallam Shekarau “Daman abunda ake fada, na yana yi wa PDP aiki, ya tabbatar da gaskiya.”
Mallam Ibrahim Shekarau yayi kuka akan shugabancin kama karya na gwamnatin jihar a halin yanzu, shine ya sa yayi sauyin sheka zuwa jam’iyyar PDP, kuma ya kara da cewa akwai mutanen kirki, da na banza a kowace jam’iyya.