Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ziyarar Shugaba Jonathan Zuwa Adamawa ta Kawo Daidaituwa Cikin APC


Shugaba Goodluck Jonathan
Shugaba Goodluck Jonathan

Ziyarar shugaba Jonathan ta kawowa jam'iyyar APC wata nasarar bazata inda bangarorin uku da basa cudanya da juna suka daidata domin su fuskanci PDP

Ko shugaba Jonathan bai cimma wata nasara ba bisa ga ziyarasa zuwa jihar Adamawa jam'iyyar APC zata gode masa domin bangarorin da ke rikici da juna sun daidaita yayin ziyararsa da nufin kalubalantar PDP.

Ziyarar ta bude wAni sabon babi a jihar Adamawa a tsakanin jam'iyyar PDP dake mulkin kasar da kuma jam'iyyar adawa ta APC. Yanzu kusoshin jam'iyyar APC da basa dasawa da juna sun dinke barakarsu domin fuskantar PDP. Bangarorin Janaral Buba Marwa da bangaren Gunduri da na gwamnan jihar Murtala Nyako sun ce sun dinke barakarsu ne domin fuskantar PDP.

Su ma 'yan PDP sun yi taro inda suka ce su basu razana ba da hadewar bangarorin APC. Sakataren PDP a jihar Barrister A.T. Shehu ya ce duk hadewar da APC suka ce sun yi magana ce ta banza. PDP tana nan yadda take babu abun da zai razanata. Ya ce duk wani da ya yi fice a jihar ya kasance wurin tarbar shugaban kasa.

A karshen ziyarar shugaban ya koma Abuja yayin da kowace jam'iyya ke ikirarin ta samu nasara.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG