Yayin da yake jawabi a wurin taron karbar wasu 23 da suka shigo jam'iyyar shugaban ya ce tuni wasu da suka fice suka fara dawowa cikin jam'iyyar. Ya ce yana ji a jikinsa cewa wadanda suka bar jam'iyyar zasu dawo. Ya ce a duk fadin jihar Kaduna wadanda suka fice daga jam'iyyar su 37 ne kuma sun kafa kwamitin binciken musabbabin barin jam'iyyar. Ya ce kawo yanzu kusan rabinsu sun dawo.
Jam'iyyar PDP inji shugaban jam'iyya ce mai jama'a da yawa. Hayaniyar da ake yi cikinta an saba ana yin hakan tun lokacin kafata a shekarar 1999. Ko a gidan mutum a kan samu hayaniya kuma a gyara. Ya ce ko mutum daya ne ya dawo zasu karbeshi su kuma bashi hakuri.
Kan shakkar ko wadanda suka fice zasu dawo sai ya ce ko yau ma wasu sun dawo. Ya bugi kirji mutane zasu dawo har ma ya ce a zo ranar Alhamis wato gobe ke nan a ga wadanda zasu dawo.
Alhaji Yahay Aminu shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Kaduna ya ce a dimokradiya ana iya cin zabe ko a fadi da kuri'a daya tak. Ya ce a yi la'akari da mutane 23 da suka shiga jama'iyyar. Kowannensu yana da mata da 'ya'ya da 'yanuwa da masu yi masa hidima a ce sun shiga jam'iyyarsu to cigaba ne.
Onarebul Salisu A Sha'aibu Dawaki tsohon shugaban jam'iyyar Actin Party ta jihar Kaduna daya daga cikin wadanda suka shiga PDP ya ce abubuwa da yawa suka ja hankalinsu shiga PDP amma ya ce hade-haden da wasu ke yi kowa mai hankali ya san a Najeriya yau PDP ita ce kawai mafita. Shi ma Idris Inuwa shugaban Community Party ta Najeriya ya ce sun tsunduma cikin PDP.
Ga karin bayani.