Wasikar ta ce banda lokacin yakin basasa da kasar ta sukurkuce bata bata samun kanta a wani mawuyacin hali ba kamar yanzu a lokacin wannan mulkin. Cin hanci da rashawa da rashin tsaro da rashin aikin yi da yunwa sun yiwa kasar katutu. Layi Muhammed ya ce gwamnatin da ta sa mutane cikin wannan irin halin to ina sauran anfaninta.
Kan wasikar da tsohon shugaba Obasanjo ya rubutawa shugaba Jonathan ya ce ya tabo maganganu da dama da ba za'a iya kawar da kai game da su ba. Don haka majalisun kasar su yi bincike su kuma dauki matakan tsige shugaban. Da aka fada ma Layi Muhammed cewa baya ganin bukatarsu tamkar wuce makadi da rawa ne sai ya ce ba haka ba ne. Dokar kasa ta ce idan shugaban kasa ya aikata ba daidai ba ya kuma saba wa dokar kasa to dole a tsige shi. Laifukan da ya zana a wasikarsa ya ce laifuka ne da suka cancanci a tsigeshi.
Na farko ya ce shugaban baya ganin majalisun kasa da martaba. Shugaban ne wanda yake boye masu cin hanci da rashawa. Shugaba ne wanda ya kasa tabbatar da tsaro da dai sauransu. Don haka babu wani abun jira ga wannan shugaban illa a tsigeshi.
To sai dai mai magana da yawun jam'iyyar PDP Olise Metuh a taron manema labarai da ya yi a Abuja ya bayyana bukatar jam'iyyar APC da rashin tunane da hangen nesa. Ya ce irin wadannan kalamun su ne ka iya tada zaune tsaye. Shi ma a wasikar da ya rubutawa Muryar Amurka mai magana da yawun shugaban kasa Dr Reuben Abati ya ce kalamun APC tamkar cin amanar kasa ne kuma jam'iyyar APC ta kuka da kanta idan gwamnatin tarayya ta kuduri daukar mataki a kanta. Ya ce a cikin wasikar da ta rabawa kafofin labarai bata bada hujja daya kwakwara ba dalilin da take bukatar a tsige shugaban.
Ladan Ibrahim Ayawa nada rahoto.