Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da PDP


Tinubu, hagu, Atiku dama (Hoto: Facebook: Kashim Shettima/Atiku Abubakar)
Tinubu, hagu, Atiku dama (Hoto: Facebook: Kashim Shettima/Atiku Abubakar)

Yayin da jam’iyyar APC mai mulki ke kokarin ganin ta ci gaba da zama a kan karagar mulki, ita kuwa PDP kokari take ta ga mulkin ya dawo hannunta.

Yayin da zaben 2023 ke ci gaba da karatowa a Najeriya, manyan jam’iyyun siyasar kasar, na ci gaba da neman makusar junansu don neman goyon bayan masu kada musu kuri’a.

A watan Fabrairun badi Najeriya za ta gudanar da zaben shugaban kasa.

Yayin da jam’iyyar APC mai mulki ke kokarin ganin ta ci gaba da zama a kan karagar mulki, ita kuwa PDP kokari take ta ga mulkin ya dawo hannunta.

PDP ta mulki Najeriya tsakanin 1999 zuwa 2015, kafin APC ta karbe mulkin.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wanda dan jam’iyyar APC ne, zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu a badin.

Tinubu Ya Zama wa APC Kadangaren Bakin Tulu – PDP

Cikin wata sanarwa da ta fitar a karshen makon da ya gabata, jam’iyyar PDP ta kwatanta dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu a matsayin “kaya” ga jam’iyyar.

“Asiwaju ya zama babban jidali ga APC, ya kamata ya sani cewa, sanadiyyarsa, miliyoyin mambobin jam’iyyar ta APC sai ficewa suke yi a sassan kasar suna komowa PDP. Cikin wata guda da ya shude, sama da ‘yan APC miliyan biyar ne suka koma PDP.

“Dalilin hakan shi ne, ‘yan Najeriya sun gano cewa PDP da dan takarar shugaban kasarta, Atiku Abubakar, su ne mafita ga kasar, yayin da ake kallon Asiwaju a matsayin “wata sabuwar matsala daga APC.” Sanarwa ta PDP mai dauke da sa hannun Sakataren yada labaranta na kasa Depo Ologunagba ta ce.

PDP Ba Tsarar APC Ba Ce – Tinubu

Yayin kaddamar da yakin neman zabensu na tsarin bi gida-gida a Abuja a karshen makon da ya gabata, Tinubu ya fadawa mambobin jam’iyyar ta APC cewa, kada su damu da kurarin da PDP ke yi, saboda PDPn ba za taba iya hada kanta da APC ba, domin matsayinsu ba daya ba ne a idon ‘yan Najeriya.

Tinubu ya kara da cewa, abin mamaki ne a ce har yanzu jam’iyyar PDP na raye, duk da irin zargin da ake cewa gwamnatinsu ta gaza tsawon shekara 16 da ta kwashe tana mulki.

“Wadannan mutane ne da ke ta fada akan shugabancin jam’iyyarsu, suna ta laluben hanya. ai matsayinmu da su ba daya ba ne, mun fi su dabara, mun muka san hanya.

“Kada mu damu kanmu da PDP – (Poverty Development Party) wato jam’iyyar masu bunkasa talauci. Mu sassauta, yanzu ba lokacin yakin neman zabe ba ne, za su ji daga garemu.” Tinubu ya fadawa mambobin jam’iyyar ta APC kamar yadda gidan talabijin na Arise TV ya ruwaito.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG