Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sama Da Mutane Miliyan Biyu Ke Bukatar Ruwan Sha A Birnin Aleppo Na Kasar Syria


A jiya Talata ne majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa sama da mutane Miliyan biyu a birnin Aleppo na Syria basu da hanyar samun ruwan sha ko wutar lantarki, ta kuma yi kira da a dakatar da fadan da ake don samun damar gyara da kuma samar da kayayyakin jin ‘kai.

Lokacin da yake magana da manema labarai a birnin New York mai kula da raba kayayyakin jin ‘kai na majalisar dinkin duniya Stephen O’Brien, yace “yanzu haka muna da kayayyakin jin ‘kai a hannumu, muna jiran aikawa da abinci da magunguna har ma da Mai na injinan samar da wutar lantarki.”

Hukumomin majalisar dinkin duniya sunyi ta kira da samar da dokar tsagaita wuta ta kwana biyu a duk mako, domin samar da kayayyakin jin ‘kai da mutanen birnin Aleppo ke bukata da kuma kwashe su, amma hakan bata cimma nasara ba. O’Brien, yayi kira ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya da ta yi amfani da ikon ta domin tabbatar da faruwar hakan.

Hare haren da aka kai cikin makon nan ya lalata hanyoyin samun wutar lantarki da ruwan sha na Aleppo, yayin da hare hare na baya bayan nan ya katse manya manyan hanyoyin da ke shigar da kayayyakin more rayuwa, wanda ya hakan ya kara mayar da hannun agogo baya ga matsalar da mutane ke fama da ita, da bukatar kayayyakin jin ‘kai.

XS
SM
MD
LG