Wanda 'yan wasan Rasha su ka yi ta yi, wanda ya zarce hukuncin rage ma kasar yawan shiga gasar guje-guje da tsalle-tsalle na lokacin bazarar "summer," wadda ake yi a Rio de Janeiro.
Kwamitin Gasar Olympic ta Kasa da Kasa ya amince da shigar 'yan wasan Rasha 271 a gasar ta Rio, wadanda kashi 70% na 'yan wasan kasar kenan.
To amma Kwamitin Gasar Kasa Da Kasa Na Nakasassun ya yi tir yadda 'yan wasan Rasha su ka yi ta amfani da kwayoyin kara kuzarin, ciki har da lokacin gasar kasa da kasa ta nakasassu wadda aka yi a Sochi na kasar ta Rasha a 2014, sannan ta hana 'yan wasan Rasha shiga gasar da za a yi daga 7 zuwa 18 na watan Satumba, wadda ita ma za a yi a Rio.