Da ya ke jawabi ga miliyoyin jama'a a wani gagarumin gangamin da aka yi a birnin Istanbul, Erdowan ya kuma lashi takobin zakulo wadanda ke da hannu a yinkurin juyin mulkin da aka yi a watan jiya da kuma "duk wata hukumar da ke bayansu."
Erdogan, wanda ya yi jawabin daga wani mambari mai tsawon mita 60, wanda aka lullube da wata babbar tutar kasar da kuma hotunan mutumin da ya kafa Turkiyya, Mustafa Kemal Ataturk.
Shugabannin manyan jam'iyyun adawa biyu sun tsaya ganga da Shugaba Erdogan. Amma bai gayyaci Shugaban jam'iyyar HDP mai ra'ayin Kurdawa ba.
"Ranar 15 ga watan Yuni ta bude kofar sulhu." a cewar Shugaban jam'iyyar Republican Kemal Kilicdaroglu. Wanda ya kara da cewa, "Idan za mu iya fadada wannan to za mu iya gadar ma 'ya'yanmu kasar Turkiyya shahararriya."
Firaminista Binali Yildirim ya hana bayyana ra'ayin siyasa a jiya Lahadi din a wani yinkuri na karfafa cigaba. "Batun kasa guda, tuta guda, al'umma guda kuma jaha guda zai rinjayi komai a tsawon lokacin wannan gangamin," a cewarsa.