Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaukaciyar Guguwa Mai Suna Earl Tayi Barna A Yankin Gabar Mexico


Belize Hurricane Earl
Belize Hurricane Earl

Gocewar kasa, wadda mahaukaciyar guguwa mai suna "Earl" ta haddasa, ta hallaka mutane 38 a yankin gabar Mexico da Caribean, a cewar jami'ai a jiya Lahadi.

Yawancin mace-macen sun auku ne a jihohin Veracruz da Puebla da ke gabas, inda ruwa kamar da bakin kwarya ya mirgino duwatsu da laka daga kan tuddai, su ka yi ta binne gidaje tare da toshe hanyoyi.

Guguwar 'Earl' ta abka ma Belize da Guatemala da kuma kudancin Mexico a makon jiya da karfin mataki na daya na mahaukaciyar guguwar, wadda karfin ta ya yi ta raguwa lokacin da ta ke dosar doron kasa.

A halin da ake ciki kuma, masu yin hasashen yanayi sun yi gargadin yiwuwar mahaukaciyar guguwar ta far ma kudu maso yammacin Mexico tun daga Manzanillo ta Kudu zuwa Cabo Corrientes a daidai lokacin da guguwar Javier ke kadawa bisa Tekun Pacific.

XS
SM
MD
LG