Sai dai masu lura da al’maura sun ce yadda dakarun Rasha da na gwamnati suka ke ci gaba da kai hare-haren sama babu kakkautawa, alama ce da ke nuna cewa ‘yan tawayen sun samu nasara akan dakarun kasar da na Rasha.
Wannan lamari kuma ana tunanin zai iya kawo cikas kan tattaunawar da Amurka da Rasha ke yi kan ‘yan tawayen a kasar ta Syria da yaki ya daidaita.
Kungiyar nan ta Jabhat al- Nusra da ta balle daga kungiyar Al Qaeda a watan da ya gabata ta bayyana cewa ita ce ta jagoranci kutsen da mayakanta suka yi.
Ita dai Amurka ta gayawa Rasha cewa ta rika tantance tsakanin kungiyoyin ‘yan tawaye da kuma mayakan jihadi a duk lokacin da za ta kai hare-haren sama.
Sai dai ita Rasha a nata bangaren ta yiwa mayakan kudin goro ne, inda ta ce duk wadanda su ke yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bashar Al –Assad, ‘yan ta’adda ne a wurinta.