Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tattalin Arzikin Amurka Ya Yi Zaburowar Bazata


Dalar Amurka
Dalar Amurka

Sabanin hasasoshin da aka yi ta yi a baya, tattalin arzikin Amurka ya yi wani irin zaburan da ya bai wa masana mamaki. Tuni Shugaba Donald Trump ya ce manufofinsa ne su ka haddasa wannan cigaban.

Tattalin arzikin Amurka ya yi saurin cigaban da ba a ga irinsa ba tun shekaru hudu da su ka gabata, a cikin watannin Afirilu da Mayu da kuma Yuni na bana.

Rahoton Ma'aikatar Cinakayya na jiya Jumma'a ya ce tattalin arzikin Amurka, wanda shi ne ya fi girma da kuma karfi a duk duniya, ya karu da kashi 4.1% a ma'aunin shekara-shekara a zango na biyu na kwata.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce rage harajin da ya yi da kuma manufofinsa na cinakayya, su ne su ka haifar da wannan cigaban da tattalin arzikin Amurka ya samu.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG