Wanda suke zargi da kurakurai da kin basu bayani dagane da binciken da kwamitin bincike na mussaman kan rawar da kasar Rasha ta taka a zaben shugan kasar Amurka a shekarar 2016.
Rosenstein ne ke sa ido kan binciken tunda da shugabansa Jeff Sessions, ya cire kansa daga batun. Rosenstein ya nada tsohon daraktan hukumar binciken FBI Robert Mueller a matsayin mai bincike na mussaman, kuma kawo yanzu tawagar binciken Muller ta tuhumi mutane 32, ciki har da waddanda suka yi wa shugaba Donald Trump aiki a kamfen sa.
Trump da mukarrrabansa sun sha cewa binciken da ake yi bita da kulli ne kawai kuma Trump ya sha karyata cewa tawagar kamfe dinsa ta hada kai da Rasha don su taimake shi a zaben 2016.Wata mai magana da yawun ma'aikatar shari'a ta gayawa VOA cewa ma'aikatar bata da abin da zata ce kan takadar da aka rubuta na tsige Rosenstein.
Facebook Forum