Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Ta Yi Watsi Da Tayin Tattaunawa Kai Tsaye Da Amurka Ta yi


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban rundunar sojojin kasar Iran ya yi watsi da tayin tattaunawa kai tsaye da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na cewa ashirye yake ya gana da shugabannin kasar Iran din

A daya bangaren kuma, shugaban rundunar sojin kasar Iran, ya yi watsi da tayin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi, na tattaunawa kai-tsaye da shugabannin Iran, yana mai cewa Tehran ba za ta taba amincewa ta gana da abin ya kira “Babban Shaidani ba”

Babban kwamandan rundunar tsaro da ake kira Islamic Revolutionary Guards a turance, ko kuma IRGC a takaice, Mohammad Ali Jafari, ya bayyana hakan a wata budaddiyar wasika da aka wallafa shafin kamfanin dillancin labaran Fars News Agency na gwamnatin Iran.

A cikin wasikar, Jafari, ya kara jaddada cewa Iran ba za ta taba tattaunawa da Amurkan ba, wacce ya wa lakabi da babbar shaidaniya, domin dogaro da addinin Islama da kasar ta Iran ta yi, ya sa “ta sha banban da sauran kasashe masu mika wuya ga Amurka” kamar yadda ya rubuta.

Kwamandan rundunar sojin ta Iran ya kuma kwatanta shugaba Trump a matsayin “dan koyon shugaba” wanda burinsa na ganin jami’an Iran sun nemi a tattauna da su, zai bi shi “har kabari.”

Jafari, shi ne babban jami’i a kasar ta Iran da ya mayar da martani kai-tsaye ga tayin da shugaba Trump ya yi a ranar Litinin, a wani taron manema labarai a Fadar White House, inda ya ce zai tattauna da shugabannin Iran kan shirin nukiliyanta, ba tare da gindaya wasu sharudda ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG