Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Ya Umurci Koriya ta Arewa Ta Yi Koyi Da Vietnam


Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo

Mike Pompeo sakataren harkokin wajen Amurka ya umurci Koriya ta Arewa ta kulla yarjejeniya da Amurka kamar yadda Vietnam ta yi bayan yakinta da Amurkan

Jiya Lahadi sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya bukaci kasar Korea ta Arewa data kwaikwayi kasar Vietnam ta kula sabuwar dangantaka da Amurka, kamar yadda Vietnam din tayi fiye da shekaru arba’in da suka shige bayan karshen yakin Vietman da Amurka.

Mr Pompeo yayi wannan furucin ne a Hanoi baban birnin kasar Vietnam bayan ziyarar kwanaki biyu da ya kai Korea ta arewa don tattaunawa da nufin ganin Korea ta arewa ta wargaza shirin ta na nukiliya.

Yace daidaita dangantaka tsakanin Amurka da Vietnam na shekaru ashirin da uku, ya kamata ta zama sheda ga shugaban Korea ta arewa cewa Amurka zata iya kula dangantaka mai kyau da amfani da tsafin abokan gaban ta.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG