Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Bada Sanarwar Kakabawa Iran Takunkumi


Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo

Sabon takunkumi da Amurka ke shirin kakabawa Iran zai shafi bangaren makamashi da harkokin bankin kasar

Amurka ta bada sanarwar shirye shiryen sake aza takunkunmin masu gauni akan bangaren makamashi da harkokin bankin kasar Iran, tana mai fadin cewa akwai bukatar gwamnatin Iran ta canja halayar ta ko kuma take taken ta, ta zama kamar sauran kasashen duniya.

Direktan tsara manufofi a ma’aikatar harkokin wajen Amurka Brian Hook shine yayi wannan furuci jiya litinin a tattauna da yan jarida.

Mr Hook ya bukaci kasar Iran ta mutunta abubuwan da aka nema ta yi domin ta zama abinda yace, kamar sauran kasashen duniya.

Yace a ranar shidda ga watan gobe na Augusta Amurka ke shirin aza takunkun farko. Wadannan takunkunmin zasu auna bangaren cinnikayar motoci da zinari da kuma wasu muhimman karafa. Yace sauran takunkunmin kuma Amurka zata aza su ne a ranar hudu ga watan Nuwamba idan Allah ya kai. Su kuma zasu auna bangaren makamashi da man fetur da kuma harkokin banki.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG