Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alamu Koriya ta Arewa Na Ci Gaba Da Inganta Makaman Ta


Kwanan nan shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Koriya ta Arewa ta sha alwashin dakatar da ayyukan ta na Nukiliya sai ga shi ana zargin da kwai lauje cikin nadi.

Ana nuna damuwar ganin Korea ta Arewa tana kara karfi, maimakon warware cibiyar ayyukanta na Nukliya da makamai masu linzami. Sakataren ma'aikatar harkokin wajen Amurka Mike Pampeo a wannan makon zai kai ziyara ta 3 zuwa Pyongyang.

Ziyara tasa ta biyo bayan tattaunawar da aka yi ranar lahadi a yankin Koriya da aka haramta gudanar da ayyukan soja, tsakanin jakaden Amurka a kasar Filipin Sung Kim da yan kasar Koriya ta Arewa.

Wannan shine karo na farko da jami'an kasar Amurka da na Koriya ta Arewa suka gana tunda shugaban Amurka ya tattauna da takwaran aikinsa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un a ranar 12 ga watan Yuni a Singapore.

Trump a kwanan nan ya bayyana cewa babu sauran wata barazana ta makaman Nukliya daga Pyongyang biyo bayan nasarar da aka samu akan tattaunawarsu da shugaban kasar Koriya ta arewan.

Hotunan tauraron dan Adam da jami'an lekan asirin Amurka sun karyata wannan tabbacin inda suka nuna shaidar ayyukan kwanan nan a wurare da daman na sirri a Kasar Koriya ta Arewan wanda ke da alaka da samar da ma'adanin Uranium don kera Makaman Nukliya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG