Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iraniyawa Sun Bankawa Ofishin Jakadancin Saudiyya Wuta


Malamin 'Yan Shi'ar Da Saudiyya Ta Kashe, Sheikh Nimr al-Nimr
Malamin 'Yan Shi'ar Da Saudiyya Ta Kashe, Sheikh Nimr al-Nimr

A daren jiya Iraniyawa sun bankawa ofishin jakadancin Saudi wuta a Tehran, don nuna rashin jin dadin kashe wani Shehin Malamin Shi’a da masarautar Saudi ta yi.

Shima Babban Jagoran Addinin kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei yace kasar Saudiyya zata fuskanci tsarkakekken martanin ramuwar gayya akan zartar da hukuncin kisan da suka yiwa Sheikh Nimr al-Nimr.

Yace “Ko ya iza jama’a daukar mataki ko shirya tsare-tsaren da suka ce, to wannan kisan an yi shi ne kawai don yana kalubanatar Sarakunan Saudiyya a addinance”.

Rundunar sojojin juyin-juya halin Iran ma sun fidda wata sanarwa cewa, kashe al-Nimr rashin Imani ne, kuma zai zama sanadin faduwar Sarautar Saudiyya. An kashe Malamin ne a jiya, cikin mutane 47 din da Saudin ta yankewa hukuncin kisa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG