Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran ta zargi Saudiya da kai hari da gangan kan ofishin jakadancinta dake Yamal


Tutocin Saudiya da Iran
Tutocin Saudiya da Iran

Rikicin diflomasiya tsakain Saudiya da Iran ya kara tsamari yau Alhamis biyo bayan harin da Iran ta zargi Saudiya da kaiwa kan ofishin jakadancinta a Yamal

Kasar Iran ta zargi Saudiya da kai hari da gangan akan ofishin jakadancinta dake kasar Yamal.

Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran Hossein Jaber Ansari yace harin da Saudiya ta kai kan birnin Sana'a fadar gwamnatin Yamal ya karya dokokin kasa da kasa da suka kare ma'aikata da ofisoshin jakadanci. Yayi kalamun nasa ne ta kafar talibijan.

Yace "Saudiya ce ke da alhakin lalata ginin jakadancin kasarsa tare da jikata ma'aikatan." To saidai a cikin bayaninsa bai kayyade yawan mutanen da suka ji ciwo ba ko yawan barnar da harin ya yiwa ofishin.

Saudiya dai tana kai hari ta jiragen sama a Yamal a matsayin goyon bayan da take baiwa dakarun da suke fafatawa da 'yan shiyar Houthi da Iran ke marawa baya. Kawo yanzu Saudiya bata ce komi ba kan zarge-zargen.

Kazalika yau Alhamis majalisar zartaswar Iran ta haramta shigo da duk wasu kaya daga kasar Saudiya kamar yadda wata sanarwa da gwamnatin ta fitar. Haka kuma ta haramtawa 'yan kasar yin balaguro zuwa Makka da sauran kasar ta Saudiya.

Matakan da Iran ta dauka sun biyo bayan da Saudiya ta yanke huldar diflomasiya da kasar ta Iran makon jiya biyo bayan wani mugun zanga-zanga da iraniyawa suka yi a harabar ofishin jadancin Saudiya dake Tehran. Kashe shugaban 'yan shiya na Saudiya Shaikh Nimr al-Nimr da kasar ta yi ya harzuka masu zanga-zanga a Tehran babban birnin Iran.

Tuni wasu kasashen Larabawa suka yanke huldar diflomasiya da Iran a matsayin nuna goyon bayansu ga Saudiya. Wasu kasashen kuma sun rage dangantakarsu da Iran din.

XS
SM
MD
LG