Kasar Saudi Arabia ta yanke huldar diplomasiyya kwana guda bayan da masu zanga zanga a birnin Tehran suka far ma ofishin jakadancinta domin nuna fushinsu bisa kashe wani fitaccen Malamin Shi’a da Saudiyan ta yi.
A wani martini da kamafanin dillancin labaran Iran na IRNA ya dauka, mataimakin ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir Abdollahian, ya soki Saudiyya kan matakin da ta dauka na ranar Lahadi, inda ta kashe Sheikh Nimr-al-Nimr.
Sai dai a daya bangare kuma ministan ma’aikatar harkokin wajen Saudi, Abdel-al-Zubair ya ba da umurnin cewa dukkanin jamai’an dimplimasiyyan Iran da su fice daga kasar cikin sa’oi 48.
A cewar al-Jubeir, Saudiya ba za ta amince da ci gaba da kai hare-hare akan ofishin jakadancinta ba, domin hakan ya sabawa dokar kasa da kasa.
An dai kashe Malamin Shi’an ne tare da wasu mutane 46 a kasar ta Saudiyya, lamarin da ya janyo kakkausar suka daga kasashe duniya