Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Ta Gwada Makami Mai Linzami


Canadian Prime Minister Justin Trudeau greets performers upon arrival at Clark International Airport in Clark, Pampanga province north of Manila, Philippines, Nov. 12, 2017.
Canadian Prime Minister Justin Trudeau greets performers upon arrival at Clark International Airport in Clark, Pampanga province north of Manila, Philippines, Nov. 12, 2017.

Iran ta sake gwada makami mai linzami mai matsakaicin zango sabanin yarjejeniyarta da Majalisar Dinkin Duniya

Rahotanni a kafofin yada labarai na Amurka sun ce Iran tayi gwajin wani makami mai Linzami mai matsakaicin zango, matakin da ya kasance bijirewa ce ga kudurori biyu na Majalisar Dinkin Duniya wadanda suka haramtawa kasar yin irin wadannan nan gwaje-gwaje.

Jami'an Amurka wadanda suka yi magana bisa sharadin da ba za'a bayyana sunayensu ba, sun gayawa kafofin yada labarai na Amurka cewa, Iran ta yi gwajin ne ranar 21 ga watan Nuwamba, kuma makamamin ba ketare hurumin Farisan ba.

A cikin watan Oktoba Iran tayi gwajin makami mai linzami mai cin dogon zango, wanda ya janyo kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya tayi Allah wadai da matakin. Har yanzu kwamitin sulhun yana shawarwari kan irin martani da zai dauka kan wancan gwajin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG