Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Nijar Sun Soke Dokar Da Ta Haramta Tafiya Ci-Rani


'Yan Cirani Jamhuriyar Nijar
'Yan Cirani Jamhuriyar Nijar

Sojojin da ke mulki a Jamhuriyar Nijar sun soke dokar da ta taimaka wurin rage kwararar ‘yan kasashen Yammacin Afirka zuwa Turai musamman mazauna karkara wadanda ke fama da matsin tattalin arziki da suka dade suna dogara da ci-rani.

Dokar dai, doka ce da ta sha tada jijiyoyin wuya tsakanin kungiyoyin farar hula da gwamnatin wancan lokacin ta Issoufou Mahamadou wacce tayi ta shan suka a ciki da wajen kasar har ta kai ga kungiyoyin shigar da karar gwamnatin Nijar a gaban kotun kasa da kasa dake kare hakkin bil Adama.

An yi dokar ne a shekara ta 2015 wadda ta haramta jigilar 'yan ci-rani ta cikin Nijar ba bisa ka’ida ba don zuwa kasar Libiya da nufin zuwa Turai.

A hirarshi da Muryar Amurka, Sanussi Mahaman, dan fafutukar farar fulla na m62, ya ce a lokacin a aka dauki dokar, akwai kungiyoyin hadin gwiwar kasashen Turai, kuma su ne suka tursasa wa Nijar ta dauki matakin.

Adadin 'yan ci ranin da ke shiga ta Nijar wacce ita ce kasar da aka fi ratsawa da yada zango a tafiya zuwa Turai ya ragu a tsawan shekaru takwas, saboda wannan dokar ba tare da la’akari da halin da dokar zata jefa mutane ba.

Amadu Umaru shugaban kungiyar na daga cikin wadanda su ka yi watsi da safarar 'yan ci-rani bayan kafa dokar, ya kuma ce a yanzu haka hanya ta bude, kuma duk wanda ke son komawa na iya komawa.

Rashin aikin yi ya karu a birane irinsu Agadas wanda wuri ne da yayi suna ga masu tafiya ta cikin hamadar Sahara.

To sai dai kungiyoyin farar hula a Agadas na fatan ganin an yi tsarin da zai sanya kowa ne bangare ya anfana da juna.

Sakamakon wannan dokar Tarayyar Turai ta fitar da biliyon biyar na Yuro a wasu kasashen Africa domin kawo karshen matsalolin dake tattare da ci rani. Sai dai tsamin dangantaka dake tsakanin sojoji da tarayyar Turai bayan juyin mulki, ya sanya sabbin mahukuntan Nijar sake yin nazari akan alakar kasar Nijar da kasashen na yamma wadanda su ka yi Allah wadai da juyin mulki na ranar 26 ga watan Yulin wannan shekarar.

Saurari rahoton Hamid Mahmoud:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG