Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Mulkin Sojin Nijar Ta Soke Dokar Da Ta Rage Safarar Bakin Haure Zuwa Turai


Tsohon Hoto: Shugaban Mulkin Sojan Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahmane Tiani, dama
Tsohon Hoto: Shugaban Mulkin Sojan Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahmane Tiani, dama

Rashin aikin yi ya yi kamari a wurare kamar tsohon birnin Agadez wanda ya zama babbar mashigar yankin Sahara da masu safarar ke ratsawa da bakin haure.

Majalisar mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta fada a ranar Litinin cewa ta soke dokar da ta haramta yin kaura wacce ke taimakawa wajen rage kwararar mazauna kasashen yankin yammacin Afirka zuwa nahiyar Turai a cewar Reuters.

Mazauna yankin Hamada kan amfana da aikin safarar mutane wajen samun kudaden shiga.

Dokar, wadda ta haramta safarar bakin haure ta cikin Nijar, an amince da ita ne a watan Mayun 2015, yayin da adadin mutanen da ke bi ta Tekun Bahar Rum daga Afirka ya kai wani matsayi mafi girma da ta kafa tarihi, lamari da ya haifar da rikicin siyasa da na jin-kai a Turai, inda gwamnatoci suka fuskanci matsin lamba kan su dakatar da kwararar bakin hauren.

Gwamnatin mulkin soja Nijar wacce ta karbe mulki a watan Yulin da ya wuce, ta soke dokar a ranar Asabar, inda ta sanar da hakan a ranar Litinin a gidan talabijin din kasar.

Gwamnatin sojan dai na sake nazarin alakarta da tsoffin kawayenta na yammacin duniya wadanda suka yi Allah wadai da juyin mulkin, sannan tana neman goyon baya a cikin gida, ciki har da al’ummomin yankin Hamadar arewacin kasar da suka fi cin gajiyar kaurar.

Yawan bakin da ke bi ta kasar Nijar, wacce ta kasance babbar hanyar da masu kaura ke bi ke da ke kudancin Hamadar shara, ya ragu matuka tsawon shekaru saboda dokar.

Sai dai sauyin ya janyo cikas ga al’umomin garuruwa da kauyukan da ke cin gajiyar safarar bakin haure wadanda kan sayar musu da kayan gyaran motoci da man fetur da ba su makwanci.

A nata bangaren, kungiyar Tarayyar Turai ta kaddamar da asusun kusan dala $5.5B don tallafawa Afirka a 2015, da nufin kawar da musabbabin yin kaura, amma da dama na ganin bai wadatar ba. R

Rashin aikin yi ya yi kamari a wurare kamar tsohon birnin Agadez wanda ya zama babbar mashigar yankin Sahara da masu safarar ke ratsawa da masu kaura.

Har yanzu ba a ji abin ko shugabannin kasashen Turai sun yi maraba da wannan labari ba da irin tasirin da matakin zai iya yi kan masu kaura zuwa Turai.

Amma wasu sun yi maraba da shi. Andre Chani ya kasance yana samu dubban daloli a wata na tuka bakin haure ta cikin sahara kafin ‘yan sanda su kwace manyan motocinsa a 2016. Yana shirin sake fara kasuwancinsa da zarar ya samu kudi.

“Zan sake farfado da harkar,” Chani ya ce ta sakon tes da ya turo daga Agadez a ranar Litinin. “Muna murna sosai.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG