Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Shiri Na Yiwa Ma’aikatar Pentagon Kutse A Yanar Gizo


Hackers
Hackers

Jiya Larabane ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta baiwa masu kutse a yanar gizo katin gayyata, inda ta baiwa Amurkawa wanda basu taba yin wani laifi ba damar yiwa shafinta kutse, a wani gwaji da take na tabbatar da tsaro ga shafukanta.

Wannan shine karon farko da gwamnatin Amurka ta bata irin wannan shiri.

Da yake bayyana shirin a wata sanarwa sakataran tsaron Amurka Ash Carter, yace “ina da kwarin gwiwar cewa wannan shiri zai kara karfin tsaron ma’aikatarmu ta yanar gizo, ya kuma inganta tsaron kasar mu.”

Shirin mai suna “Hack the Pentagon” an dai shirya zai fara aiki farkon watan gobe idan Allah ya kaimu, kuma zai iya yiwuwa a bayar da kyautar kudi ga wadanda suka gano a ina matsalar shafin intanet din ma’aikatar tsaron ta Pentagon ta ke.

San nan kuma shirin ba zai hada da bayyana muhimman sirrin shafin yanar gizon ba, musammam ma ta bangaren sinadaren kimiyyarsa ba.

Da zarar an fara shirin, za a kula da duk masu kutsen da ke cikin shirin, haka kuma za a barsu su gano duk wata kofar rago dake shafin wannan ma’aikata. A cewar Pentagon.

XS
SM
MD
LG